Complete Tafseer Sheikh Ja'afar Mahmud 2003 Part 1 Apk Download for Android

Complete Tafseer Sheikh Ja'afar Mahmud 2003 Part 1 Apk Download for Android

Complete Tafseer Sheikh Ja'afar Mahmud 2003 Part 1 Apk Download for Android

Complete Tafseer Sheik Jafar Mahmud Adam 2003 series Part 1. Sheik Jafar Tafsir

***Tarihin Sheikh Jafar Mahmud Adam***

An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam a garin Daura, a shekara ta 1962 (ko da yake wani lokacin yakan ce 1964).

Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, a wurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini. 

Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin su, wanda kuma shi ne musabbabin zuwansa Kano. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano.

Tun kafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Jaafar ya riga ya fara haddar Alkur'ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978.

Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani mai girma, kasancewarsa mai sha'awar
ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980. Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (Egyptian
Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru
na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu. Haka ya rika yin wannan karatu guda biyu: Waccan makarantar ya je ta da daddare bayan sallar isha'i, waccan kuma ta koyo harshen larabcin da yamma. Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983. Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar
GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988. 

A shekara ta 1989, malam jafar ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci, A Oundurman Sudan. Sannan kuma, kafin rasuwarsa, ya riga ya yi nisa wajen karatunsa na digiri na uku, wato digiri da digirgir (PhD), a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da take Sokoto.
---------------------------------------------------------
Category : Music and Audio App
Last Updated :  17 July, 2019
Current Version : 3
Requirements : 4.1+
Developer : Abyadapps

No comments: