Magana Jarice Yaro Bada Kudi A Gaya Maka: Story 2 Apk

Magana Jarice Yaro Bada Kudi A Gaya Maka: Story 2 Apk

Magana Jarice Yaro Bada Kudi A Gaya Maka: Story 2 Apk

Karanta cikakken littafin magana Jarice littafi na biyu. Magana Jari ce littafi na biyu wallafar Alhaji Dr. Abubakar Imam kamfanin Gaskiya Zaria.

Wannan littafi, `Magana Jari ce, 2', yana cikin littattafai guda uku da Alhaji Abubakar Imam ya rubuta a cikin wata shida na zamansa a Zariya a shekarar 1936. Dalilin za6o shi kuwa ya rubuta wadannan littattafai shi ne ya shiga wata gasa to rubutun littafi a shekarar 1933 ya kuma ci nasara da littafinsa na farko 'Ruwan Bagaja'. 

MAGANA JARICE LITTAFI NA BIYU - Yaro Bada Kudi A Gaya Maka!

Domin samun littafin magana jari ce part 1 sau ku duba Manhajja mai suna magana jari ce 1 (Littafi na Farko).

A cikin wannan manhajja akwai cikakkun labaru kamar haka:

☆ Magana Jari Ce

☆ Yaro Tsaya Matsayinka Kada Zancen 'Yan Duniya Ya Rudeka

☆ Baruan Arziki Da Mugun Gashi

☆ Kalala Da Kalalatu

☆ Yusha'u Na-Narimi Dutse Baka Fargaba

☆ Mara Gaskiya Ko Cikin Ruwa Yayi Jibi

☆ Ba Gaskiya Bace Abar Bida Ga Shariah, Kai Dai A Samo Sa'a

☆ Sarkin Noma Da 'Yayansa

☆ Da Muguwar Rawa Gwamma Kin Tashi

☆ Jimrau Dan sarkin Noma Na Biyu

☆ Labarin Wani Makaho

☆ Kosau Dan Sarkin Noma Na Fari

☆ An Ki Cin Biri An Ci Dila

☆ Gamuwar Kosau Da Jimrau Da Nomau

☆ Jarrabawar Da Aka Yiwa Sarkin Barayi Nomau

☆ Wadansu Madinka Su Uku

☆ Kuda Wajen Kwadayi Akan Mutu

☆ Yaro Bari Murna Karenka Ya Kama Zaki

☆ Kukan Kurciya Ma Jawabi Ne, Mai Hankali Ke Ganewa

☆ Labarin Wani Sarki Da yaronsa

☆ Zafin Nema Baya Kawo Samu

☆ Allah Na Taimakon Wanda Ya Taimaki Kansa

☆ Ja'iru 'Dan Sama Jannati

☆ Wadansu 'Yan Kama Da 'Yan Sama Jannati

☆ Sarkin Farisa Da Wani Bahindi

☆ Labarin Wadansu Samari Su Uku

☆ Kama Da Wane Ba Wane Ba Ne

☆ Labarin Sarki Kamaruzzaman Dan Sarki Shahruzzaman

☆ Amjadu Da Asadu

☆ Kyale Maketaci Yayi Ta Halinsa, Kome Ta Jima Zamani Na Nan

☆ In Maye Nada Hankali Baya Fid Da Maitarsa A Fili

☆ Iya Gani Iya Kyalewa

☆ Rana Ta karshe

An haifi Alhaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.) N.N.M.C. a shekarar 1911 a cikin garin kagara sa'an nan tana cikin lardin Kwantagora, yanzu kuwa Jihar Neja. Ya Yi makaranta a Katsina Training College kuma ya kama aikin malanta a Makarantar Midil to Katsina a shekarar 1932. Yana da shekara 22 ya rubuta `Ruwan Bagaja'. Ganin kwazonsa wajen Raga labari mai ma'ana ya sa Dr. R.M. East shugaban Offishin Talifi na Zariya ya roki a ba da shi aro daga Katsina ya yi aikin rubuce rubuce a Zariya. Bayan ya koma Katsina aka bi shi da rokon ya kara rubuta wasu , littattafan. A can ya rubuta 'Karamin Sani kukumi' cikin 1937. A cikin shekara 1938 sai Gwamnan Kaduna ya roka a dawo da Imam Zariya a koya mashi aikin edita ya zama editan jaridar farko to Arewa. Shi ne ma ya rada mata suna `Gaskiya Ta Fi Kwabo' aka fara bugawa a watan Janairu na shekara 1939.

Ya yi shekara 12 yana wannan aiki na edita har ma ya rubuta wani littafi a lokacin `Yakin Duniya Na Biyu' watau `Yakin Hitila' da ya ba suna `Tafiya Mabudin Ilmi'. Wannan littafi ya ba da Iabarin tafiyarsa tare da wasu editoci na jaridun Africa to Yamma zuwa Ingila a jirgin ruwa a shekara 1943.
---------------------------------------------------------
Category : Entertainment App
Last Updated :  22 July, 2019
Current Version : 3
Requirements : 4.1+
Developer : Abyadapps

No comments: