Tarihin Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah (SAW)

Tarihin Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah (SAW) Apk

Tarihin Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah (SAW) Apk

Wannan application yana dauke da tarihi na Annabi Mohammead (S.W.A), wanda wani shahararen marubucin tarihi ya wallafashi da harshen larabci.Shine aka fassara shi zuwa harshen hausa domin amfanarwa ga al'umar Hausawa wadan da ke neman ilimi akan cikakken tarihin Manzon Allah (S.W.A).
Littafin ya kunshi gundarin rayuwar Manzon Allah tun daga kan haihuwar sa, da kuma irin gwagwarmayar da yasha kafin a fara saukar masa da wahayi. Littafin bai tsaya nan ba kadai, ya kara bamu asali da kuma tarihi na musulunci tun daga kan annabi na farko, wato annabi Adam (AS) zuwa sauran annabawa, a takaice shi dai wannan littafi yafi bada karfi akan kafuwar musulunci da kuma rayuwar Annabi Mohammad (S.A.W).
Ina fatan wannan application wanda akayi shi don saukin amfani zai zamo abin amfanarwa ga al'umar musulmi.
Don Allah idan har kaji dadin wannan application kayi kokari ka yadashi don wasu suma su amfana.

Takaitaccen tarihin manzon Allah SAW.

Manzo Muhammad Al-Habib ɗan ʿAbdullahi (Sallallahu ʿalaihi wa sallam).

Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muɗallabi ɗan Hashimi ɗan Abdu-Manafi ɗan Ƙusayyi ɗan Kilabi, Sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam, (Harshen Larabci: Abūl-Qāsim Muḥammad ibn ʿAbd Allāh ibn ʿAbd al-Muṭṭalib ibn Hāshim ibn ˁAbd Manāf ibn Qusayy ibn Kilāb) nasabarsa maɗaukakiya tana tuqewa zuwa ga Annabi Ibrahim, alaihi salatu wassalam.

Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu (Āminah) 'yar Wahbi ɗan Abdu-Manaf ɗan Zuhrata ɗan Kilabi (Radhi Allahu anha). Alkunyarsa: Abul-Qasim, Abu Ibrahim.

Laqabinsa: Almusxafa yana da sunaye da suka zo a cikin Kur'ani mai girma kamar, Khataman nabiyyin, da Al'ummi da Almuzzammil da Almuddassir da Annazir da Almubin da Alkarim da Annur da Anni'ima da Arrahma da Al'abdu da Arra'uf da Arrahim da Asshahid da Almubasshir da Annazir da Ad'da'i da sauransu.
---------------------------------------------------------
Category : Books and Reference App
Last Updated :  17 July, 2019
Current Version : 1.0
Requirements : 4.0+
Developer : uyaapps

No comments: