English Hausa Kamus Apk free Download for Android

English Hausa Kamus Apk free Download for Android

English Hausa Kamus Apk free Download for Android

This app is an offline English to Hausa comprehensive bilingual Dictionary (or Kamus in Hausa) containing thousands of British and American English words/phrases and Abbreviations.

Each words came along with parts of speech.

We specified British IPA pronunciation of any English word for those wishing to know how to pronounce a particular word.

We provide English to Hausa bilingual usage sentences,

Scientific words, medical words, geology, geography, biology, anatomy, chemistry, physics, literature, computing, psychology and linguistics words were included and precisely translated to Hausa.

Wannan manhaja ce mai aiki ba tare da internet ba mai dauke da kamus na turanci da Hausa na shafin www.kamus.com.ng

Wannan kamus ne dake ɗauke da ma'anar kusan kowace kalmar turanci a cikin harcen hausa. Abubuwan da wannan kamus yake ɗauke dasu sune kamar haka:

1. Ma'anonin kalmomin turancin ingilishi a cikin harshen hausa.
2. Ajin kalmomi (Parts of speech)
3. Haruffan furuci (IPA pronunciations)
4. Misalan yanda ake anfani da kalmomin turanci a cikin jimla. Kalmomin turanci suna da ma'anoni mabanbanta kuma ana anfani dasu a yanayi daban daban. Don haka sanin ma'anar kalma kawai bazai sa mutum ya iya yin magana da turanci ba har sai ya san yanda ake anfani da ita a cikin jimla; a saboda haka ne yasa kusan kowace kalma muna sanya ta a cikin jimla tare da fassara ta da Hausa domin mutane susan yanda ake amfani da ita.
5. Fassarar misalan jimlolin turanci cikin harshen Hausa (kuma na tabbata wannan shine kawai kamus na Hausa dake ɗauke da irin wannan fassarar)
6. Kalmomin darussan kimiyya (biology, medical, chemistry, physics, anatomy da dai sauran su) kuma na tabbata wannan shine kawai dictionary na hausa da zaka samu a halin yanzu wanda yake ɗauke da sahihiyar fassarar kalmomin waɗannan darussan
7. Kalmomin darussan linguistics da psychology
8. Sahihiyar fassara. Wannan kamus ya banbanta da sauran manhajojin kamus da kuke downloading domin kuwa na ɗauki tsawan shekaru biyar ina sanya kowace kalma ce ɗaya bayan ɗaya bayan na tabbatar da sahihancin fassarar ta. Na fara wallafa wannan kamus ne a shafin yanar gizo na http://kamus.com.ng kafin daga bisani na samar da manhajar shi ta Android.
9. Babu tamkar shi a halin yanzu. Wannan kamus shine kawai wanda wani bahaushe ko mai jin hausa ya wallafa, don kuwa duk wani Hausa dictionary da zaka samu a cikin wannan store batun wannan Turawa ne suke wallafa shi ta hanyar yin amfani da na'urar fassara yaruka (machine translation) hakan yasa zaku samu kurakurai masu tarin yawa a cikin su. Domin babu yadda zaka haɗa fassarar na'ura da kuma ta mutum.

Idan an samu wata matsala gurin aiki da wannan manhajar ko kuma an samu wasu kalmomi da ba su sai a sanar damu.
 ---------------------------------------------------------
Category : Education App
Last Updated :  08 January, 2020
Current Version : 2.2
Requirements : 4.0+
Developer : Shamsuddeen Zakariya

No comments: