Rayuwar Annabi Muhammadu SAW & Sahabai & Matayensa Apk

Rayuwar Annabi Muhammadu SAW & Sahabai & Matayensa Apk

Rayuwar Annabi Muhammadu SAW & Sahabai & Matayensa Apk

Wannan application yana dauke da Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Sallam Daga Haifuwa Zuwa Jana’iza, da RAYUWAR ANNABI (S.A.W) A CIKIN WATAN AZUMI da Rayuwar Annabi (S.A.W) A Lokacin Aikin Hajji da Matsayi Sahaba A Lokacin Annabi SAW & Bayansa da kuma Falalan Uwayen Muminai (Matan Manzon Allah SAW) wanda wasu Shahararen marubuta na tarihi suka wallafashi da harshen larabci. Shine aka fassara shi izowa harshen hausa domin amfanarwa ga al'umar Hausawa wadan da ke neman ililmi akan cikeken tarihin Manzo Allah (S.A.W).

Littafin ya kunshi gundarin rayuwar Manzon Allah tunda ga kan haihuwar sa, da kuma irin gwagwarmayar da yasha kafin a fara saukar masa da wahayi. Littafin bai tsaya nan ba kadai,ya kara bamu asali da kuma tarihi na mussulunci tunda daga kan annabi na farko, wato annabi Adam (AS) zuwa sauran annabawa a takaice.shi dai wannan littafi yafi bada karfi akan kafuwar musulunci da kuma rayuwar Annabi Mohammad (S.A.W).
ina fatan wannan application wanda akayi shi don sauwakin amfani zai zamo abin amfanarwa ga al'umar musulmi.
Don Allah idan har kajin dadin amfani da wannan application kayi kokari ka yadashi don wasu suma su amfana.

Takaiccen tarihin manzon Allah.

Manzo Muhammad Al-Habib ɗan ʿAbdullahi (SAW).

Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muɗallibi ɗan Hashimi ɗan Abdu-Manafi ɗan Ƙusayyi ɗan Kilabi, Sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam, (Harshen Larabci: Abūl-Qāsim Muḥammad ibn ʿAbd Allāh ibn ʿAbd al-Muṭṭalib ibn Hāshim ibn ˁAbd Manāf ibn Qusayy ibn Kilāb) nasabarsa maɗaukakiya tana tuqewa zuwa ga Annabi Ibrahim, alaihi salatu wassalam.

Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu (Āminah) 'yar Wahbi ɗan Abdu-Manaf ɗan Zuhrata ɗan Kilabi (Radhi Allahu anha). Alkunyarsa: Abul-Qasim, Abu Ibrahim.

Laqabinsa: Almusxafa yana da sunaye da suka zo a cikin Kur'ani mai girma kamar, Khataman nabiyyin, da Al'ummi da Almuzzammil da Almuddassir da Annazir da Almubin da Alkarim da Annur da Anni'ima da Arrahma da Al'abdu da Arra'uf da Arrahim da Asshahid da Almubasshir da Annazir da Ad'da'i da sauransu.

Tarihin haihuwarsa: 17 Rabi'ul Auwal Shekarar Giwa (571m) bisa mash'hurin zance gun Ahlul Baiti (a.s), an ce, 12 ga watan da aka ambata. Wurin haihuwarsa: Makka. Aikoshi: An aiko shi a Makka 27 Rajab yana xan shekara arba'in.

Koyarwarsa: ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da 'yan'uwantaka da rangwame na gaba xaya ga wanda ya shiga musulunci, sa'annan ya kafa shari'a maxaukakiya da dokoki na adalci da ya karvo daga wajan Allah su kuma musulmi suka karva daga gare shi.
 ---------------------------------------------------------
Category : Lifestyle App
Last Updated : 16 March, 2020
Current Version : 2.8
Requirements : 4.1+
Developer : first-rate-apps

No comments: